Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Tsarki, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad bayan haka, Wannan dan littafi yana bayani ne game da tsarki a addinin Musulunci cikin harshen Hausa, domin amfanin Musulmi kasancewar wannan hanya mafi sauki wajen yada sako a cikin fadin duniya ga miliyoyin mutane, sabanin tsohuwar hanya ta buga littafi a rarraba shi, da fatan za'a samu Wani wanda zai dauki nauyin wannan aiki a matsayin Sadakatul Jariya domin cigaba da gudanar da wannan aiki na alkhairi ta yadda wata rana zai zamanto akwai tarin littattafai masu yawa cikin harshen Hausa.